Yanzu Yanzu : An sake Sace ɗaliban Jami’ar Abia Da ƙarfin bindiga

Wasu ƴan bindiga da ba’a san ko suwaye ba, sun sace wasu daliban Jami’ar Jihar Abia da ke Uturu, waɗanda daren ranar Larabar data gabata.

An daiyi garkuwa da ɗaliban ne yayin da suke tafiya a kan bas watau akan hanyar Okigwe zuwa Uturu.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Abia, John Kalu ne, ya tabbatar da faruwar hakan a wata sanarwa a ranar da aka fitar a ranar Alhamis. Sanarwar tace:

“Bayanin farko da muka samu ya nuna cewa ɗaliban suna tafiya ne a ƙaramar mota daga Okigwe zuwa Uturu tsakanin karfe 7 na yamma zuwa 8 na dare, lokacin da suka yi karo da wasu ƴan ƙungiyar da ke ɗauke da muggan makamai waɗanda suka korasu zuwa cikin dajin da ke kusa, kuma sun haɗa su tare da wasu matafiya da ba a gano su waye ba.

“Biyu daga cikin ɗaliban sun yi nasarar tserewa daga maharan yayin da wasu ɓarayin ke cigaba da tsare ɗaliban a wani wurin da har yanzu bamu kai ga ganowa ba.

“Muna aiki tare da gwamnatin jihar Imo da kuma hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki a jihohin biyu domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban da aka sace da sauran su.

“Muna shawartar jama’a da kuma jama’ar ABSU da su kwantar da hankulansu domin ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da lafiyar waɗanda abin ya shafa.

“Babu wani mai aikata laifi da ke aiki a tsakanin mu da zamu bashi damar tsere wa adalci yayin da muke ɗaukar aikin kare rayuka da dukiyoyin ƴan jihar Abia da masu ziyarar jihar da matuƙar muhimmanci.”

Wannan shi ne kame-kame na baya-bayan da aka kuma kitsawa tun bayan sace ɗaliban kwalejin Tarayya ta Afaka a watan Maris.

Inda aka sace dalibai 23 da ma’aikata daga Jami’ar Greenfield da ke Kaduna a ranar 20 ga Afrilu.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *