YANZU-YANZU: Manya Manyan agenda guda 14 da sabon shugaban ƴan sandan Najeriya zai fuskanta

Usman Alkali Baba Sabon shugaban yan sandan Najeriya

A kwanakin baya ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sahale sutale Adamu Muhammed da naɗa Usman Alkali Baba amatsayin Shugaban yan sandan Najeriya.

To saidai, sabon shugaban na ƴan sandan yazo ya haɗu da ƙalubale kala kala wadanda suka haɗa da, garkuwa da mutane, rikicin makiyaya da manoma, rashin walwala na yan sanda, sace sace da dai sauransu.

A ƙoƙarin da Usman Alkali Baba yake na ganin kawo ƙarshen matsalar tsaro, shugaban ƴan sandan Najeriyar ya fitar da sababbin agendoji har guda goma sha huɗu domin cikar wannan burin nasa. Ga jerin su:

1. Rushe kowani irin shingen bincike dake hanya a lungu da saƙon Nijeriya.

2. Janye ƴan sandan dogari daga wajen manyan mutane domin bawa kamfanunnukan aikin samar da tsaro masu zaman kansu daman walwala da bunƙasa.

3. Cire gamida zabtare albashin duk wani ɗan sanda da aka samu yaci zarafin ɗan ƙasa ba bisa haƙƙi ba.

4. Ɗaukar lawyoyi masu ilimi da gogewa a ban “shari’a da sasantawa” har guda dubu ɗaya da ɗari biyar , sannan duka za’a turawa ko wanne ofishin ƴan sanda da kuma babban ofishin ƴan sandan, a inda zasu kasance sun maida hankali wajen harƙallolin Shari’a, bincike na laifi, shawarwarin Shari’a da kuma gabatar da masu laifi.

5. Siya da kuma saka na’urar daukan hoto a duk wani dakin binciken da ƴan sanda suke dashi.

6. Gina sababbin ɗakunan bincike a kowacce jiha guda talatin da shida da muke dasu haɗi da Abuja. Aikin waɗannan ɗakuna na bincike zai haɗa da, gwajin ƙwayoyin halitta na waɗanda ake zargi, zanen hannu, gwajin jini, da duk wani abu mai ruwa ruwa dake jikin ɗan Adam.

7. ƙaddamar da tsarin siyowa ƴan sanda motoci, wanda zai zama haɗin gwuiwa ne da kamfanin Motoci na Innoson da PAN. (Yan sanda zasu biya kuɗin kaɗan kaɗan har zuwa tsawon shekaru ashirin)

8. Gaggauta gyarawa da sake tsarin makarantun ‘yan sanda da tsarin karatunsu.

9. Duk wani canjawa ɗan sanda wajen aiki idan za’ayi, za’a yi shine tare da bashi abinda zai kaisa, gamida guzurin wajen zama.

10. Za’a dinga bawa ƴan sanda sababbin kayan aiki guda biyu haɗe da takalma biyu biyu ga duk wani jami’in ɗan sanda duk shekara.

11. Za’a ƙara adadin kuɗin gudanarwa na ofishin ƴan sanda, inda za’a dinga biyansu kai tsaye, domin gudanar da aikace aikacensu.

12. Duk wata za’a dinga duba gamida ƙididdige ko wani cell sau biyu, wannan jan aikin zai zamto haɗin gwuiwa ne wanda za’a gudanar tare da wakilai daga reshen NBA da kuma ɗunƙulin taron alƙalai.

13. Bada beli da zarar lauyoyi sun isa dakin yan sanda, musamman ga waɗanda suka iso wajen da kayan aikin lauyoyinsu kuma basa iƙirarin kare rajin haƙƙin bil’adama.

14. Samar da Shayi na rage ƙiba da teɓa, ga ƴan sanda masu ƙaton ciki.

Saura dame? Fatan jaridar Mikiya shine, waɗannan agendoji da aka gindaya su tabbata, domin samun al’umma haɗaɗɗiya da zata kasance ta barranta daga duk wani nau’i na laifi.

Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *