Yanzu-yanzu: Rundunar Sojin Sama ta yi ruwan bama-bamai a yankin Bello Turji

Wani jirgin yaki mallakar rundunar sojojin saman Najeriya NAF ya kaddamar da wani sabon hari a yankin shugaban ‘yan bindigar Zamfara, Bello Turji.

Dan bindigan da ya yi kaurin suna ya tsallake rijiya da baya a wani harin bam da aka kai masa a gidansa da yammacin ranar Asabar.

Wata majiya ta shaida Jaridar Dailytrust cewa jirgin yakin ya koma yankin ne da misalin karfe tara na safiyar yau Litinin, inda ya jefa bama-bamai akalla biyu.

A halin da ake ciki, wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan sansanin Turji ne sun kai farmaki kan matafiya a kan hanyar Sokoto zuwa Gusau a Shinkafi, da safiyar Litinin.

Wani mazaunin garin Shinkafi, Murtala Wadatau, ya ce ‘yan bindigar sun tare hanya a Kwanar Badarawa da Birnin Yero.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *