YANZU-YANZU: Yan bindiga sun kashe yan sanda guda uku, sunyi awon gaba da makamansu a jihar Ebonyi.

An ruwaito wasu ‘ƴan bindigar da ba’a san ko su waye ba da alhakin kai hari ga wasu yan sanda dake aikin tsaida motoci su duba akan hanyar Onuebonyi, hanyar Nwwzenyi ta Abakalikin jihar Ebonyi, kamar yadda jaridar Dailypost ta ruwaito.

Rahoton ya bayyana cewa, lamarin maras daɗin ji, ya afku ne a daren laraba, yayin da ƴan bindigar kawai suka buɗewa jami’an ƴan sandan irin salon harbin nan na kan mai uwa da wabi.

A nan take, ‘ƴan sanda uku suka ce ga garinku nan, su kuma ɓata garin sukayi awon gaba da makamansu.

DSP Odah Loveth Obianuju itace mai magana da yawun ƴan sandan jihar Ebonyi, ta faɗawa manema labarai cewar:

“Lamarin ka iya zama gaske, amma bamu tabbatar a hukumance ba kawo wannan lokacin da ake haɗa rahoton nan”.


Ita kuwa mataimakiyar Kwamishinan yan sanda bangaren aikace aikace, tana wajen da abin ya faru domin tabbatar da ummul aba’isin abinda ya wakana. Inda ta ƙara da cewa:
“Zai iya kasancewa gaskiya ne, amma muna jiran sakamakon bincike ne, wanda yanzu haka masu bincike na can wajen bincikawar domin samo cikakken bayani akan dalilin faruwan haka”.
Ta kuma yi alkawarin sake tuntubar wakilin majiyar mu, bayan kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *