Wasu ƴan Bindiga a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna sun nemi a kawo musu dafaffen abinci a matsayin kuɗin fansa bayan sunyi garkuwa da wasu mutane.
An tabbatar da cewa ƴan Bindigar sun shiga halin rashin tabbas tun bayanda Gwamnatin Jihar Kaduna ta kulle kasuwannin yankunan a yunƙurin shawo kan matsalar tsaro a yankin.
Ɗaya daga cikin matasa mazauna yankin na Birnin Gwari mai suna Babangida Yaro, ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewa tun bayan da aka kulle kasuwanni a yankin nasu, a duk loƙacin da ƴan Bindigar suka yi garkuwa da wani mutum babu abinda suke tambaya a matsayin fansa sai dafaffen abinci.
Ya ƙara da cewa “dakatar da sayarda man-fetur ya taimaka wajen rage zirga-zirgar ƴan ta’addan, kuma yanzu sun samu sauƙin hare-hare a yankunan nasu.
Har’ilayau, matashin ya bayyana cewa a yanzu idan ƴan bindigar suka sace mutum uku a gona, sai su aika ɗaya daga ciki domin ya je cikin gari ya nemo musu abinci sakamakon babu halin da zasu iya tattaunawa ta hanyar wayar salula da iyalan waɗanda suka sace.
A ƙarshe, matashin ya bayyana cewa dakatar da zirga-zirgar abin hawa a yankin na Birnin Gwari ya taimaka wajen daƙile ayyukan ta’adanci amma, a gefe guda suma mutanen gari suna fama da matsin rayuwa sakamakon matakin.
~Rahoto | Ya’u Sule Tariwa