
Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya Janar Lucky Irabor, ya bayyana a jiya cewa ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda a hukumance zai baiwa rundunar sojin ƙasarnan damar daukar matakin da ya dace a kansu.
Irabor, wanda ya yi magana a lokacin da yake gabatar da shirin ‘Good Morning Nigeria’, a gidan talabijin na Najeriya, NTA, ya ce sojoji za su gyara dabarun su, idan aka yi la’akari da sabon ci gaban da aka samu, ya kara da cewa za a baiwa masu laifin wahala har“ hancin su ya zubar da jini kamar yadda suke so. “.
Ya ce: “Batun mayar da ‘yan fashin a matsayin ‘yan ta’adda labari ne da ke faranta rai. Wannan ya kasance abin da muke so.
“Abin da ake nufi shi ne dabarunmu, da hanyoyin da muka yi amfani da su wajen yakarsu tabbas dole ne su canza kuma shi ya sa, na yi imanin za a sami ci gaba, na tabbata za ku karanta menene sakamakon waɗancan ayyukan.
A ranar 5 ga watan Janairu ne gwamnatin tarayya ta fitar da wata sanarwa, inda ta bayyana ‘yan fashi a matsayin ‘yan ta’adda.
Matakin na gwamnati, ya zo ne wata guda bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ayyana ayyukan dukkan kungiyoyin ‘yan bindiga a ƙasarnan a matsayin ayyukan ta’addanci.
Allah yakara ilmin Mai anfani