Zamu tsige Buhari indai yanayin tsaro bai gyaru ba – Dan Majalisa

Wani ɗan majalisa mai wakiltar Mazabar Tarayyar Jos ta Kudu da Jos ta Gabas a Majalisar Wakilai, Dachung Bagos ya ce Majalisar Tarayya za ta duba yiwuwar tsige Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari idan har bangaren zartarwa bai kawo maslaha ba akan mummunan yanayin tsaro da yake daɗa ɓacewa a cikin kasar nan.

Ɗan majalisar ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin daya baƙunci wani shiri a matsayin bako na musamman da ake yi a gidan talabijin na “Channels” mai suna “Sunrise Daily”.

Idan za’a iya tunawa ne dai, a laraban nan ne, aka rantsar da wani kwamiti mai ɗauke da mutane arba’in domin samo mafita mai daurewa akan ƙalubalen tsaro da addabi ƙasar nan.

Inda a watan Mayu ne, ake fatan zai gabatar da taron tattaunawa akan tsaro na kwana huɗu.

A lokacin da ake gabatar da shirin ne, Bagos ya faɗa cewar, idan har kwamitin ya yi bincike ya bada mafita amma kuma ɓangaren zartarwa baiyi amfani da mafitar da suka bayar ba, bayan wani ɗan lokaci, za’a soma bin tsarin da doka ta tanadar domin cire shugaban ƙasa.
A cewar sa:

“Idan har ɓangaren zartarwa baiyi amfani da mafitar da kwamitin zai kawo ba, to zamu soma bin tsarin tunbuƙe Shugaban ƙasa ne kawai.

“Ina tabbatar muku da cewa, muna da ƙarfin iko da doka ta bamu domin mu tunbuke shi, in har bazai iya kare rayuwa da kadarorin ƴan Najeriya ba. Inji sa

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *