Zamu Tsige Shugaba Buhari Idan Matsalar Rashin Tsaro Yayi Kara Yi gaba bayan taron tsaro ~ inji dan majalissa Dachung Bagos

Wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Jos ta Kudu /Jos ta Gabas a majalisar wakilai, Dachung Bagos ya ce majalisar kasa za ta fara shirin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari idan tsaro ya tabarbare a watan Mayu.

Dan majalisar ya ce majalisar ta kaddamar da kwamiti mai mambobi arba’in da zai duba tsabagen kalubalen tsaro a kasar.

Ya kuma ce, tsige Shugaban zai kasance mafaka ta karshe da Majalisar Dokoki ta Kasa za ta yi, wanda zai zo idan bangaren zartarwa ya kasa aiwatar da kudurorin taron kolin tsaro da zai fito daga kwamitin Majalisar a watan gobe.
Bagos ya fadi haka ne a yayin wani shirin gidan talabijin na Channels TV, Sunrise Daily, a ranar Alhamis.

“Babu wani memba da abin bai shafa ba sakamakon rashin tsaro. Ba zan iya zuwa mazaba ta ba saboda kashe-kashe nan da can. Kuna da mambobi da yawa kamar haka.

Bagos ya ce “Idan har bangaren zartarwa ba zai aiwatar da komai ba bayan wannan mafaka ta karshe to muna kira da a tsige Shugaban. Muna da ikon tsige Shugaban idan har ba zai iya ci gaba da tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya ba.”

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *