Labarai

Tshohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ba da gudummawar N200m ga Al’ummar jihar don bukukuwan Sallah

Spread the love

Alhaji Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 200 ga al’ummar jihar domin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah.

Malam Yusuf Idris, sakataren yada labaran jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Danfulani.

Danfulani wanda shi ne Shugaban kwamatin rabon kayayyakin ya ce wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da ‘yan uwa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da mata da kungiyoyin matasa da kuma kungiyoyi.

“Sauran wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da marayu da marasa galihu, malaman addinin Musulunci, masu aikin yada labarai, da masu gudanar da shafukan sada zumunta da dai sauransu.

“Karimcin na da nufin taimaka wa mutane su yi bikin Eid-el-Kabir mai zuwa na 2023 cikin sauki. Tuni dai kwamitin ya fara rabon kudaden ga duk wadanda suka ci gajiyar kudin,” inji Idris Danfulani.

Danfulani ya mika godiyarsa ga Matawalle da wannan karimcin da yayi, ya kuma bayyana hakan a matsayin abin da ya dace da domin zai kawo karshen tabarbarewar tattalin arziki a tsakanin al’ummar jihar musamman a matakin kasa.

Ya ba da tabbacin cewa kwamitin zai tabbatar da cewa duk wadanda aka yi niyya sun sami wannan karimcin kafin ranar Laraba.

NAN

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button