Rahotanni

Tsohon Gwamnan Jihar Ogun Ya Bayyana Albashin Da Ake Biyansu Sannan Yace Ya Kamata A Rage Musu Albashin.

Spread the love

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Otumba Gbenga Daniel ya bayyana albashin da aka rika biyansa lokacin yana gwamna.

Ya bayyana hakane a wani Bidiyon hirar da aka yi dashi wanda ya watsu sosai. Gbenga Daniel ya zama gwamnan Ogun daga shekara 2003 zuwa 2011.

Yace a jiharsu Dubu Dari 5 ake biyan gwamna a matsayin Albashi sannan kuma Dubu Dari 5 din ake biyansa idan ya sauka a matsayin fansho.

Yace bai san abinda ake biyan sauran jihohi ba dan ya ji cewa akwai jihohin da ake biyan gwamnonin fiye da haka kuma ana gina musu gida a Abuja a saya musu Motan hawa amma yace shi ko daya bai samu ba.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button