Labarai

Tsohon Shugaban Fansho, Maina, Yafito Daga kurku-Kun, Kuje

Spread the love

Kotu Ta saki tsohon Shugaban fansho Abdulrashid Maina, watanni tara da tsare shi bisa wasu zarge-zarge goma sha Biyu Da’akeyi Masa, Na halasta kudin haram.

Abdulrashid Maina, yasamu fitowa daga kurku-kun kuje, Bayan Mai Shari’a Justice Okon Abang, yabada Umarnin tsare shi a, 25th October 2019, Lokacin da jami’an Tsaro suka kama shi tare da Dan sa Faisal, Lokacin da Hukumar EFCC take Masa zarge-zargen wadaka da kudaden gwamnati.

Lauyan sa, Adeola Adedipe, ya fadawa Jaridar NAN Cewa wannan Al’amarine me kyau, Wanda Kuma, zai basu damar cigaba da Kare Maina, a, gaban kotu.

Abdulrashid Maina, a, kwanakin baya de Sunan Shi ya janyo Cece Kuce Sakamakon yanda A kace yadawo har, an mayar dashi mukamin sa, Kafin daga Bisani Gwamnatin tarayya ta, bukaci a, Bincike shi, inda daga Bisani akace yakoma kasar Dubai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button