Tun Farko Mahaifiyar Darkta Ashiru nagoma itace ta hanamu mu taimaka Masa mu kaishi Asibiti ~Inji Ali Nuhu
Majiyarmu Kan Batun Rashin lafiyar tsohon darakta Ashiru nagoma Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu damar tattaunawa da fitaccen jarumi a masana’antar (Kannywood) Alhaji Ali Nuhu da kuma shugaban Hukumar Tace fina-finai na Jihar Kano, Ismail Na Abba Afakallah dangane da batun tsohon darakta, Ashiru Na Goma da ke fama da rashin lafiyar taɓin hankali a halin yanzu.
A cikin tattaunawar da mu ka yi da Ali Nuhu, ya musanta zarge-zargen da ake yi musu na watsi da Ashiru Na Goma bayan ya gamu da rashin lafiya. “Tsawon shekaru da su ka wuce, mun yi ƙoƙarin kai Ashiru Na Goma Asibitin da za a riƙa kula da shi har zuwa lokacin da Allah zai ba shi lafiya amma mahaifiyarsa ta ce sam ba ta yarda ba, ɗanta lafiyarsa ƙalau babu wanda zai kai mata shi asibiti”. Cewar Ali Nuhu.
Ali Nuhu ya kuma ƙara da cewa bayan rasuwar mahaifiyar Ashiru Na Goman sun cigaba da wancan yunƙuri na kai shi asibitin amma nan ma ƴan uwansa su ka hana. “Ƴan uwan Ashiru Na Goma su ma sun ce ba su yarda mu kai shi asibiti ba bayan rasuwar mahaifiyarsa, amma tunda su ne ahalinsa na jini babu yadda mu ka iya ala dole mu ka haƙura da kai shi asibitin nema masa magani, amma duk da hakan ba mu ƙyale shi kara zube ba, mu na tallafa masa domin ni har gidana ya na zuwa ina kuma kyautata masa”. Inji Ali Nuhu
Shi ma a nasa tsokacin a ya yin tattaunawarmu da shi, shugaban Hukumar tace fina-finai na Jihar Kano, Ismail Na Abba Afakallah, ya bayyana cewa Ashiru Na Goma ya gamu da wannan iftila’i ne tun kafin shi ya hau kan wannan matsayi, kuma yanzu tunda har ƴan’uwansa sun amince a nema masa magani to za su kafa kwamiti na musamman a matsayin gidauniyar kulawa da Ashiru Na Goma.
Afakallah ya bayyana cewa Ashiru Na Goma ya ba da gagarumar gudunmawa ga masana’antar Kannywood a lokacin da ya ke da lafiya saboda haka a yanzu su ma za su yi iya ƙoƙarinsu domin ganin sun temaka masa.
Da ya ke tsokaci game da zargin da ake yi musu na ƙin taimakawa masu buƙata kuwa, Na Abba Afakallah ya bayyana cewa al’ada ce a wannan masana’antar kafa gidauniya domin tallafawa mutanensu da su ka gamu da jinya gami da tallafawa iyalansu “Ba ƴan fim kaɗai ba, har ma da mutanen gari mu na tallafa musu a lokacin da su ke buƙatar taimako. Misali, ko da Sani Garba SK mun kaiwa iyalansa gudunmawa, akwai mutane da dama da su ka gamu da jarrabawa a wannan masana’anta da wajenta kuma mun tallafa musu, al’amari ne idan ka yi saboda Allah ba dole sai ka faɗawa duniya ba”. Cewar Dakta Sarari.
Tunda farko, Afakallah ya bayyana cewa babu wani mutum da zai so wani ya shiga cikin wata jarrabawa. Daga ƙarshe ya kuma yi addu’a Allah Ya ba wa Ashiru Na Goma lafiya.