Labarai

Tun Tuni Yakamata Gwamnatocin Baya Sucire Tallafi, Amma Saboda Basu Da Karfin Zuciyar Yi Suka Kasa, Inji Kakakin Shugaba Buhari..

Spread the love

Tarihi Ba Zai Mantae Da Sauyin Da Buhari Ya Kawo Ba~Garba Shehu.

Biyo bayan sukar da wasu ‘yan Najeriya suke yi wa Gwamnatin Tarayyar Najeriya game da tsadar kayayyaki, mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa ya ce matakan da aka ɗauka ne suka jawo hakan waɗanda kuma “suka zama dole”.

Malam Garba Shehu ya ce tarihi ba zai taɓa mantawa da sauye-sauyen da Shugaba Buhari ya kawo ba sakamakon daƙile cin hanci da rashawa a ɓangaren tallafi a kan man fetur da noma da wutar lantarki ta hanyar cire tallafin.

Sai dai cire tallafin ya jawo hauhawar farashin kaya musamman man fetur, wanda gwamnati ta ƙara zuwa naira 151 daga 148, yayin da ‘yan kasuwar da ke sayar da man suka ce sai farashinsa ya kai kusan 160 kan kowacce lita ɗaya.

Kakakin shugaban ƙasa ya ce tun tuni ya kamata gwamnatocin baya su cire tallafin amma saboda ba su da ƙarfin zuciyar yin hakan” sai suka gaza.

Za a riƙa tuna Shugaba Buhari kan yadda ya kawo cigaban ƙasa da tattalin arziki ta hanyar daƙile cin hanci da rashawa a ɓangaren kuɗaɗen tallafi, in ji Garba Shehu a cikin wata maƙala da ya wallafa ranar Lahadi.

Daga Amir Sufi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button