Tunda Ka Kasa Magana Akan Wanda Aka Yankewa Hukuncin Kisa A Kano Ba Zamu Zabe Ka Ba, ‘Yan Kudu Suka Fadawa Atiku.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Wasu ‘yan Kudancin Najeriya da dama na caccakar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019 da ya gabata, Atiku Abubakar saboda kin yin magana akan hukuncin kisan da aka yankewa matashin da yayi batanci ga Annabi(SAW) a Kano.
Sun ta yin Magana a shafukansu na Twitter inda suke neman Atikun yayi magana akan lamarin. Mun fahimci kiran ya kara kamari bayan da Atiku ya taya kungiyar Arsenal murnar nasarar da ta samu akan Liverpool jiya, inda wasu ke cewa ba akan wannan suke so yayi magana ba.
Wani me sun Nwoke NKwerre ya bayyana cewa Atiku muna so mu ji ta bakinka kan hukuncin kisa da aka yankewa matashinnan a Arewa. Wasu na ganin shirun ka kamar yana nuna ka amince da hukuncinne.
Hakanan wani me suna Malachy Odo II ya bayyana cewa Atiku na magana akan komai amma banda maganar hukuncin kisa da aka yankewq matashi a Kano saboda kalaman batanci.
Ya kara da cewa, Shirunshi ya nuna cewa shima yana da tsatstsauran ra’ayi kamarsu ko kuma baya son ya bata musu rai dan nan gaba zai nemi kuri’arsu.
Itama wata ta mayarwa Da Atiku Martani bayan da ya taya Arsenal murna da cewa, har yanzu muna jiran abinda zata ce kan maganar hukuncin kisa da akawa matashi a Kano.