Tunda na karbi Jam’iyar APC Ina kwashe kwanaki uku a jihar Yobe a kowanne wata~Mai Mala
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya mayar da martani ga masu sukarsa suna zarginshi da cewa ba ya zuwa jihar tun lokacin da ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar APC na rikon kwarya.
Akwai rahotanni da ke nuna cewa an dakatar da fayel da batutuwan da suka shafi jihar kasancewar gwamnan ya shagaltu da lamuran da suka shafi APC.
Koyaya, Gwamnan a wata hira da BBC, ya ce yana kan gudanar da ayyukansa yadda ya kamata yayin da baya jihar sa.
A cewarsa, yakan shafe kwanaki uku a wata a jihar.
Buni ya ce; “Game da batun zama a jihar, babu yadda za a yi na yi wata guda ba tare da na kwashe kwanaki uku ko hudu a jihar Yobe ba.
“Sannan kuma, ko da na koma Yobe, ba zan iya tallatawa ko bayyana a fili ba cewa yau zan kasance a Yobe gobe kuma zan tafi. ”
Gwamnan ya kuma musanta zargin cewa ya bar fayilolin ba tare da kulawa ba kuma ya maida hankali kan siyasar jam’iyya.
“Ba zan bayyana wa jama’a lokacin da na zo Yobe ko lokacin da zan tashi ba.
“Kuma a wannan zamani na fasaha, me yasa wani zai ce akwai wasu tarin fayiloli suna jira na? Tun kafin na zo nan ban san lambobi ba (na fayilolin da na kula da su). “