Labarai

Ubangiji ya barni a Raye ne kawai domin na karasa Mulki na karo na biyu ~Cewar Gwamnan Ondo

Spread the love

Gwamna Rotimi Akeredolu, na jihar Ondo, ya koma bakin aiki a hukumance bayan hutun jinya na wata daya a kasar waje.

Akeredolu wanda ya godewa ‘yan Najeriya bisa addu’o’in da suke yi na neman samun lafiya ya tabbatar musu da cewa zai rayu domin ya kammala wa’adinsa na mulki.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Rt Hon. Olamide Oladiji, ya tabbatar da komawar gwamnan a ofishinsa a Akure, babban birnin jihar.

Oladiji ya ce gwamnan ya aike da wasikar dawowar sa daga hutun jinya ga majalisar.

Ya lura cewa matakin gwamnan ya yi daidai da sashe na 190 (1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (kamar yadda aka gyara).

” Wasikar da ta samu a yau yayin zaman majalisar, gwamnan ya koma bakin aiki yau Juma’a 8 ga Satumba, 2023.

Oladiji wanda ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya dawo da Gwamnan gida lafiya, ya ce daukacin al’ummar jihar Ondo na jin dadin dawowar sa kan karagar mulki.

Ku tuna cewa a cikin wasikar Gwamna ta ranar 4 ga Yuni, 2023, ya sanar da majalisar cewa za a ci gaba da tafiya hutun jinya sannan daga baya ya tsawaita ranar 4 ga Yuli, 2023.

A halin da ake ciki, gwamnan, ya gudanar da taron masu ruwa da tsaki da ‘yan majalisar zartarwa na jiharsa, da shugabannin jam’iyyar da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button