Rahotanni

Ubangiji Yana Jarraba Mutane Ta Hanyar Wannan Annoba Ta Covid – 19 — Atiku.

Daga Miftahu Ahmad Panda

A jiya Asabar Tsohon Dan takarar Jam’iyyar Hamayya ta PDP a Zaben Da Ya Gabata Na Shekarar 2019 Alhaji Atiku Abubakar Ya Bayyana Cewar Allah Ya kawo Wannan Annoba Ta Corona Virus ne Domin Ya Jarraba Mutane.

Alhaji Atikun Yabayyana Hakanne a Sakon Barka Da Sallah Da Ya Aikewa Al’ummar Musulmin Najeriya, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasan Ya Bukaci Al’umma Dasu Mika Lamuransu Ga Allah, Tare da Gaskata Cewar Babu Wani Abu Da Zai Samesu Face Sai Da Izinin Allah.

Inda Aka jiyoshi Yana Cewa ” Dukkannin Wadannan Kuncin Rayuwa Da Muka Shiga Bazai Ragewa Azuminmu Kima Da Daraja ba, Saboda a Matsayinmu Na Al’ummar Musulmi, Munyi Imani Da Cewar Dukkannin Wani Abu Da yake Faruwa, Yana faruwane Da Izinin Allah” a cewarsa.

Sannan yakara Da Cewar ” Wannan Hali Da Muke Ciki Na Barkewar Annobar COVID – 19 Jarrabawace Daga Allah, Saboda Haka Yanada kyau Mubi Dukkannin wasu Sharudda Da Ka’idojin Da Hukumomin Da Abin ya Shafa Suka Gindaya mana”.

“Wanda Daga Cikinsu Akwai Rage Cunkoson Jama’a, Bada Tazara Tsakanin Mutane Tareda Wanke Hannu Akai – Akai, Yanada kyau Mukiyaye Wadannan Sharuddan Domin Kare Lafiyarmu data Sauran Al’umma”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button