
Jagoran jam’iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu a ranar Lahadi ya bayyana cewar, Allah ne kaɗai zai iya ɗaukar ransa tunda shi kaɗai ne kuma ke kashewa kuma yake rayarwa.
Da yake magana a wajen wata liyafar maraba da gwamnatin jihar Legas ta shirya masa, Tinubu, ya ɗauki lokaci don kama sunayen waɗanda suka dinga masa fatan alkairi tare da godewa dukkan shugabannin siyasa da ƙungiyoyin da aka wakilta a bikin maraba, yace yayi matuƙar farin ciki da dawowa gida.

Ya kuma godewa Allah da ya sadaukar da rayuwarsa har zuwa lokacin kuma ya dawo gida lafiya daga tafiyar neman magani da yayi.
Tinubu ya ce duk da tafiyarsa ta jinya ce, ba zai godewa Allah fiye da duk wanda ya halarci bikin da gamida waɗanda suka yi addu’ar ya koma gida lafiya.
Da yake bayyana cewa ranar farin ciki ce a gare shi, ya yi wa masu shirya addu’ar barka da dawowa da fatan Allah ya biya musu bukatun zuciyarsu.

Tun da farko, Mataimakin Gwamna, Dr Obafemi Hamzat da Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya ce a shirye suke su ƙara yin aiki kuma tuni sun soma aikin don tabbatar da kudirin sa , kuma haƙƙinsa na 2023.
Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru