An harbe mutum biyu wasu kuma sun jikkata yayin da ‘yan bindiga suka mamaye taron APC

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wasu mutane biyu da ake kyautata zaton mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne a jihar Ebonyi.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a unguwar Mkpuma Akataka da ke karamar hukumar Izzi a jihar.
Jaridar DAILY POST ta ce ta samu labarin cewa taron jam’iyyar APC na gudana ne da yammacin ranar Juma’a a cikin al’umma inda ‘yan bindigar suka far wa wurin inda suka bude wuta.
‘Yan ta’addan wadanda aka ce adadin su biyu ne, sun zo ne a kan babur, inda suka yi sauri su ka tashi, bayan kammala aikinsu.
An tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin da wasu biyu ke karbar kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar tarayya ta Alex Ekwueme da ke Abakaliki.
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda Chris Anyanwu ya zuwa yanzu bai samu ba.