An Naɗa Sabon Shugaban Kasa Na Riƙon Kwarya A Mali Bah Ndaw.

An naɗa shugaban riƙon ƙwarya a Mali, wanda shi zai jagoranci shirya zaɓe da miƙa mulki ga duk wanda al’ummar ƙasar suka zaɓa.

Tawagar da aka ɗora wa nauyin naɗa shugaban da zai jagoramci Mali cikin watanni masu zuwa tun bayan juyin mulkin da aka yi, sun gana a ranar Litinin inda suka naɗa shugaban ƙasar farar hula na riƙon ƙwarya da mataimakinsa.

Tsohon ministan tsaro Bah Ndaw aka naɗa a matsayin sabon shugaban na riƙon ƙwarya a Mali da kuma Kanal Assimi Goita a matsayin mataimakinsa.

Sai dai dukkaninsu tsoffin sojoji ne da suka riƙe manyan muƙaman soja a Mali.

Abun tambaya anan, shi ne ko sabon shugaban da aka nada na riƙo tsohon soja za a yi masa kallon farar hula?

Daga Amir sufi

Leave a Reply

Your email address will not be published.