An Yabawa Gwamnatin Jihar Neja Kan Korar Ma’aikata 80 A Jihar.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Jihar Neja, karkashin jagorancin Abubakar Sani Bello, ta zakulo mutane tamanin da suka karawa Kansu kudin alawus da yafi girman matsayinsu.

Tun a watan yuni ne dai gwamnatin jihar ta kafa kwamiti domin tantance ma’aikata da kula da tsarin Aikin gwamnati a jihar.

Ma’aikatan da aka samu da laifin sun fito ne daga Ma’aikatu daban daban a Jihar bisa laifin Daukar albashi ko alawus da ya girmi mukaminsu.

Idan Baku manta Ba Cikin mutane an samu mai daukar albashin Kwamishinan Gona Har Na tsawon shekaru 2 ba bisa ka’ida ba.

Har’ila yau gwamnatin Jihar ta fidda sanarwar an kama malaman Framary har guda 2886 da laifin koyarwa a makarantu alhali basuda takardun karatu.

Al’ummar jihar sun yabawa gwamnatin jihar wajen zakulo irin wayannan mutane masu cinye kudin gwamnati ba bisa ka’ida ba.

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.