Ana-wata-ga-wata: Tsaleliyar budurwa tayi waje-rod da saurayin ta, saboda yaƙi dena goyon bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal.

Wata budurwa ƴar Najeriya mai suna Blessing ta raba gari da abin ƙaunar ta bawai don yaƙi siyar mata abaya ba ko kuma yaƙi yi mata siyayyar bikin ranar haihuwar ta ba, a’a sai don kawai shi mutum ne mai matuƙar nuna shauƙi ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal dake ƙasar Ingila.

Jaridar Mikiya dai ta hango wannan matashiyar ne a dandalin sada zumunci na Twitter, ta hanyar amfani da akawun mai suna @Udanshi ta bayyana cewa, itafa yadda taga masoyin nata yana haba-haba da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, yasa hakan ko kaɗan bai mata ba, hasali ma shauƙin da yake nunawa ƙungiyar baya nuna mata.


Hakan ne, yasa tayi masa magana akan ya rage ko ya dena kwata kwata duba da naci da ƙalata da yake nunawa ƙungiyar da soyayya, amma masoyin nata ya ƙeƙashe ƙasa yace allan-baram Arsenal itace rayuwar sa, kuma a soyayyar Arsenal sune sahun farko, domin tuni ya zama ɗan amutu.

Ita kuwa a nata ɓangaren, wannan masoyiya cewa tayi, tunda yaƙi ya dena soyayya ga Arsenal, bata da wani abu daya rage face tayi bankwana da wannan alaƙa. A cewar Blessing cikin yaren bature:

“Saurayina ya ƙi ya dena son ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, saboda haka bani babu shi”. Inji Blessing

https://twitter.com/udanshi/status/1391452311583608832?ref_src=twsrc%5Etfw%7Ctwcamp%5Etweetembed%7Ctwterm%5E1391452311583608832%7Ctwgr%5E%7Ctwcon%5Es1_c10&ref_url=https%3A%2F%2Fseniorngr.com%2F2021%2F05%2F09%2Flady-broke-up-with-boyfriend-because-of-his-continuous-support-for-arsenal-club%2F
Sanarwar blessings cikin yaren Bature

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *