Covid-19 An Gudanar Da Sallar Juma’a Yau A Neja…..

A Jiya Alhamis ne Gwamnatin Jahar Neja Ta Bada Umarnin Ayi Sallar Juma’a a Fadin Jahar.

Sai Dai Gwamnatin Ta gindaya sharruda ga Masallata, Inda Tace Kowa ya Wanke Hannu, Ya Sanya Abin Kariyar Fuska Face Mask, Sannan a Bar Tazara, Kar a Tsawaita Huduba kowanne Liman Mintuna Talatiñ Aka bashi Ya Gabar da Huduba da Sallah cikin Mintuna Talatin. Kar a Wuce Karfe 2 Ba’ayi Sallah ba Saboda Akwai Dokar Zaman Gida Daga Karfe 2 zuwa 12 Na Dare. Duk Anyi Hakanne Dan Gudun Samuwar ko yaduwar Cutar Coronavirus a Jahar.

Sanarwar Wanda Sakataren Gwamnatin Jahar Kuma Shugaban Kwamitin Yaki da Covid-19 a Jahar Alh. Ahmad Ibrahim Matane Ya fitar a Madadin Gwamna Abubakar Sani Bello Lolo Na Jahar.

Wakilin Mikiya Na Jahar Ahmed T. Adam Bagas ya Ziyarci Babban Masallacin Minna (Central Mosque minna) Don Ganewa Idonsa Ga Abinda Ya Gano “Anyi Sallar Juma’a a Babban Masllaci Kuma Anbi Doka Yadda Ya kamata, Idan Zaka Shiga Masallci ‘yan Agaji Suna Tsaye Zasu Nuna Maka Ruwan Wanke Hannu, sannan Zusu Sa maka wani Abu Mai kama da Turare a Hannu sannan Kashiga Masallacin. Limamin Masallacin Sheik Ibrahim Isah Fari Ya Fara Huduba Karfe 1:12 an Tada Sahun Sallah 1:24 An Idar da Sallah 1:41. Sabanin Abaya Ana Fara Sallah 1:50 a Masallacin.”

Kawo yanzu dai Babu Ko mutum Daya da Yake Dauke da Cutar a Fadin Jahar, Sai dai An Killace Mutane 26 da Sukayi Mu’a mala da Masu Cutar a Jahar Inji Kwamishinan Lafiya Na Jahar.

Sai dai Duk wannan Matakan da Gwamnatin Ta dauka Ta yi ne Domin Gudun Yaduwar Muguwar Cutar nan Da Ta Addabi Duniya CoronaVirus.

Ahmed T. Adam Bagas

Ana Wanke Hannu Kafin Ashiga Massalacin

Leave a Reply

Your email address will not be published.