Cutar Kolara ta hallaka mutane 15 rana ɗaya cikin wani ƙauye a Jihar Kano.

Mutane 15 ne aka tabbatar da mutuwar su yayinda aƙalla kuma mutane 40 suke kwance a gadon asibiti bayan ɓullar cutar Kolara (Cholera) a ƙauyen Koya dake karamar hukumar Minjibir ta Jihar Kano.

Dagacin garin na Koya Sulaiman Muhammad shine ya tabbatarwa da manema labaru game da aukuwar al’amarin wanda yace haryanzu ba’a san abinda ya haddasa hakan ba; a gefe guda kuma ya bayyana cewa mafi yawanci ƙananan yara da mata ne cutar tafi shafi.

Babban sakataren hukumar lafiya ta Jihar Kano, Dr Hussaini Tijjani shima ya ƙara tabbatarwa da manema labaru bisa ga ɓullar cutar, wadda ta ɓulla a daren yau Lahadi.

Dr Hussaini Tijjani ya kuma bayyana cewa tuni dai hukumar lafiya ta Jihar Kano ta tura ma’aikatan lafiya zuwa ƙauyen na Kayo domin daƙile cigaba da bazuwar cutar ta Kolara.

A gefe guda kuma jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a baya-bayan nan ma an fuskanci irin wannan matsalar ta cututtuka cikin ƙauyuka da dama a faɗin Jihar Kano sakamakon amfani da gurɓataccen ruwan sha da rashin tsaftataccen muhalli.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *