Da Dumi Dumi | Sarkin Musulmi zai shirya jarabawa kan muk’amin “MURSHID” na Masallacin Abuja.


.
Rahotannin dasuke zuwa mana daga fadar mai martaba sarkin Musulmai sultan Sa’ad Abubakar na III shine fadar tare da hadin guiwar majalisar malamai ta Kasa (JNI) zata shirya jarabawa kan mukamin MURSHID na Babban masallacin Abuja da’aka aro daga saudiyya akuma karrama wata Kungiya da mukamin sabida samun maslaha. To Amma fadar tare da hadin guiwar majalisar malamai ta J.N.I sun lura shi wanda aka bawa mukamin Prof. Galadanci yakasa tafiyar da aikin sa bisa sharuddan daya amince kansu kafin abashi, kadan daga ciki shine yayi kokarin tabbatar wa dakowani Musulmi ‘yan cinsa nayin addinnin sa yanda ya fahimta a wannan masallacin, kasancewar masallacin Abuja ba mallakar wata kungiyar Addini bane mallakar Gomnatin Nigeria ne , kuma ita Gomnatin takowa ce, hakkin Gomnatin Nigeria ne da kuma nauyine akanmu mu tabbatar da anyima kowa adalci. Don haka munsami rahoto kasa da shekaru biyu da bawa shi Galadanci wannan matsayin wato ashekarar 2019 sanda wasu Musulmai suka nemi yin fahimtar su ta zikiri awannan masallacin karkashin jagorancin Babban malamin addinin musulunci Sheikh Dahiru Bauchi Amma shi Galadanci yanemi hanasu wannan ‘yancin, awancan lokacin munkirasa munja masa kunne tare dayi masa bitar ayyukansa Amma saigashi yanzu ana tsaka da ibadar watan Azumi yana kokarin kawo wata sabuwar fitina a masallacin , baza mu lamunci wannan ba, Adon haka mun amince nanda dan wani lokaci zamu dauki matakin dakatar wa akansa tare da shirya jarabawa kan matsayin dankawo wanda yake ya cancanta bayan yacika dukkan sharruddan daza agindaya. Don wajibin mune tabbatar da adalci gaduk mabiyanmu.

MUNSAMI WANNAN RAHOTO DAGA SHAFIN HAUSA ONLINE NEWS.

Ahmad Aminu Kado..

0 thoughts on “Da Dumi Dumi | Sarkin Musulmi zai shirya jarabawa kan muk’amin “MURSHID” na Masallacin Abuja.

 • April 18, 2021 at 5:09 pm
  Permalink

  Allah ya taimaka

  Reply
 • April 19, 2021 at 2:36 am
  Permalink

  Allah yakara daukaka wannan jarida tamu muna goyon baya

  Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *