Indiya: ‘Yan sanda sun kama dan Najeriya da kwayoyi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce dan Najeriyan da ake zargin ya zo Indiya ne bisa takardar bizar kasuwanci a watan Disambar 2020.

An kama wani dan Najeriya mai suna Benjamin a Indiya bayan da ‘yan sandan Chandigarh suka kwace masa giram 274 na tabar heroin.

Hindustan Times ta rawaito  cewa an kama dan Najeriya mai shekaru 25 a wani wurin duba kaya a yankin Masana’antu, Phase-2, ranar Alhamis ta hanyar Operations Cell karkashin kulawar DSP Jasbir Singh.

‘Yan sandan sun ce rundunar tana aikin sintiri ne a lokacin da suka gano wanda ake zargin.

Daga nan ne aka gurfanar da shi a karkashin dokar ta’ammali da miyagun kwayoyi (NDPS) a ofishin ‘yan sanda na sashe-31 kuma an gabatar da shi a gaban kotu ranar Juma’a.

Mista Benjamin dai zai ci gaba da zama a hannun ‘yan sanda har zuwa ranar 16 ga watan Agusta, kuma jami’an tsaro za su yi masa tambayoyi game da inda aka kai wadannan kwayoyi da kuma sauran wadanda abin ya shafa.

‘Yan sandan sun ce Mista Benjamin yana zaune ne a Tilak Nagar, Delhi kuma ya zo Indiya bisa bizar kasuwanci a watan Disamba 2020.

Kamen Mista Benjamin ya zo ne makonni bayan da aka kama wasu ‘yan Najeriya biyu kan safarar miyagun kwayoyi.

A watan Yuli, Hukumar Yaki da Muggan kwayoyi (ANC) ta ‘yan sandan Pune ta kama ‘yan Najeriya biyu tare da kwace gram 644 na mephedrone da gram 201 na hodar iblis.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Ogochukwu Emmanuel da Enebeli Omamma Vivian.

Leave a Reply

Your email address will not be published.