Jami’an Tsaro Sunyi Nasara Wurin Hana shigowa Da Miyagun Makamai cikin Kasar Nijeriya

Labari yazo daga tushen jami’i na tsaro a Nijeriya cewa, jami’an tsaro wanda suke a sashen Ingal ta garin Agadez sunyi nasara wurin hana shigowa da miyagun makamai daga Libiya wadan da aka saka cikin mota kirar Hilux wanda ta kamo hanyar zuwa Nijeriya daga kasar Libiya.

Mai bada labari wanda ya samu tattaunawa da Saharara reportersa inda yace “masu smuga din kayan yaki sun nufo hanya Nijeriya kuma ba dan jami’an tsaro ba da sun samu damar shigowa kasar

Ya kara da cewa “an kama yan smuga guda hudu wadan da suke dauke da makamai, sannan iyakar makaman da aka kwata a hannun sun hada da AK-47 guda saba’in da bakwai, RGP’s kwara bakwai, harsashi adadin dubu talatin da kuma Rokan guda biyu.

“Sun dauki hanyar Maiduguri ta cikin gari Agadas a inda aka cinma dakatar da su. Ana zargin cewa wadan nan yan smuga samar wa yan’ Boko haram makamai.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *