Jam’iyyar PDP tana neman Buhari ya gaggauta sauke Sheikh Pantami daga matsayinsa na Minista don a yi bincike kansa, akan zargin ta’addanci da wasu arna makiyan musulunci suke zargin sa

A gaskiyar magana ban taba tsanar jam’iyyar PDP ba kamar wannan karo ba, domin akan siyasar banza ana kokarin hada kai da su don a batawa Malamin mu na musulunci suna.

Duk irin kokarin da wannan bawan Allah yake yi don ganin ya kawo canji a cikin kasar nan, wasu magoya bayan jam’iyyar PDP suna ci gaba da matsawa Buhari lamba ya sauke shi tare da bincikensa kan zargin yana da alaka da kungiyoyin ta’addanci.

Hakika ko shakka babu kashi 80% na mutanen da ke a jam’iyyar PDP babu alkairi a tattare da su. Domin akan burin su na siyasa suna iya cin zarafin kowaye, kai koma addinin su ne na musulunci.

Jama’a idan zaku tuna, an taba kama shugaban kungiyar CAN ta Najeriya da jirgin sama makare da makamai zuwa kudancin Najeriya, amman har yanzu baku taba ganin wani Kirista ya fito ya yi magana kan wannan mutun ba.

Amman yau dan uwan ku musulmi wasu Kiristoci suna neman hada kai da ku don ganin an ci zarafinsa ta hanyar alakanta shi da ta’addanci.

Ya Allah ka tsinewa duk wani mutun da ake kokarin hada kai da shi don cutarda musulunci da musulmai.

Ahmad Aminu Kado…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *