Kada ku sassautawa ‘yan bindiga, Matawalle ya sanar da alkalai

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara yayi kira ga alkalai a jihar da kada su kasance masu sassauci ga ‘yan bindiga yayin shari’a.

Kamar yadda The Punch ta wallafa, Matawalle ya yi wannan kiran ne yayin da ya karba wasu mahukunta da ma’aikatan bangaren shari’a na jihar buda baki a gidansa dake Gusau.

“Ina kira ga alkalan dake shar’ar ‘yan bindiga da su yi shari’ar cike da kishin kasa kuma ba tare da wani sassauci domin kawo karshen wannan matsalar a jihar.”

Gwamnan ya sanar da ma’aikatan shari’ar cewa gwamnatinsa ta samar da sabbin ababen hawa da za ta baiwa alkalan kotun majistare da ne shari’ah a jihar.

Gwamnan ya jinjinawa ma’aikatan shari’ar a kan yadda suke aiki tare da tabbatar da alaka mai kyau tsakaninsu da masu mukamin siyasa a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa ta samu manyan nasarori sakamakon goyon baya da hadin kan da take samu ballantana a matsalalolin da kai tsaye suka shafi jama’ar jihar.

A yayin jawabi a madadin masu buda baki, kakakin majalisar jihar Zamfara, Nasiru magarya, ya jinjinawa gwamnan a kan yadda yake hada kai dasu a abubuwan da suka shafi jihar saboda hadin kai da cigaban Zamfara.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *