Rahotanni sun bayyana yadda Gwamnatin tarayya ta ayyana ƙudirin kashe biliyan 5.23 domin yiwa fadar Shugaban ƙasa kwaskwarima.
Wannan yana ƙunshe cikin wani rahoto da Jaridar Daily Trust ta wallafa ayau Lahadi؛ waɗannan kuɗaɗe suna ƙunshe cikin kasafin kuɗin bana wanda Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar a ranar Alhamis.
Har’ilayau; a cikin kasafin kuɗin na wannan shekarar da aka gabatar, an bayyana cewa Shugaban ƙasa da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo za su kashe aƙalla miliyan 457.8 domin kayan abinci da sauran buƙatun yau da kullum.
Rahoto | Ya’u Sule Tariwa