Kotu ta bayar da belin Sowore kan N20m.

Wata kotun majistare da ke zaune a Wuse Zone 2, Abuja, ta bayar da belin Omoyele Sowore, wanda ya hada kan masu shirya juyin juya halin yanzu a kan kudi Naira miliyan 20.

Sowore, Peter Williams, Sanyaolu Juwon, Emmanuel Bulus da Damilare Adenola an kama su ne a sabuwar shekara yayin jerin gwanon da Sowore ya shirya kuma ya jagoranta.

‘Yan sanda sun gurfanar da mutanen biyar a ranar Litinin da ta gabata a kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, hada taro ba bisa ka’ida ba, da tayar da hankali.

Alkalin kotun, Mabel Segun-Bello, ya bayar da umarnin a tsare su a gidan kurkukun da ke Kuje.

Amma a ranar Talatar da ta gabata, an mayar da su sashin binciken manyan laifuka da leken asiri (FCIID) bayan Sowore ya ruwaito cewa an hana su damar kula da lafiya, abinci, da ruwa.

Marshal Abubakar, lauya mai kare wanda ake kara, yayin da yake gabatar da bukatar neman belin, ya roki kotun da ta ba da belinsa ga wadanda yake karewa “a kan sanin kansu ko kuma a madadin, ba da belin a cikin mafi sauki”

Hukuncin wanda aka shirya ranar Juma’a ya tsaya ne saboda gazawar ‘yan sanda na gabatar da wadanda ake kara a kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *