A ƙalla likitoci ɗari bakwai ne suka gudanar da zanga-zangar lumana domin gwamnati ta ki rage biyansu albashi mai tsoka. A ƙasar ta Canada kowanne ƙaramin likita ana biyansa kuɗin daya kai sama da naira miliyan tara duk wata, Dan haka waɗannan likitocin su ke ganin albashin da gwamnati ta ke biyansu ya yi yawa.
Allah ɗaya gari bamban, wannan al’amarin mai kama da almara ba zai taɓa faruwa ba a ƙasata Najeriya saboda dalilai guda biyu:
1- Na farko gwamnati ba zata iya biyan ma’aikatanta kuɗaɗen da za su biya buƙatunsu ba, har ma ya yi musu yawa.
2- Sannan su ma ma’aikatan ba su da wadatar zuci ko da gwamnati zata basu fal taɓa sama su gamsu da shi.
Daga Mutawakkil Gambo Doko