Muna Neman Afuwar Yan Najeriya Kan Rashin Wutar Lantarki, “Inji Ministan Wuta Sale Mamman”

Ministan lantarki Injiya Sale Mamman ya nemi afuwar ƴan Najeriya kan rashin samun wuta yana mai cewa nan ba da jimawa ba komai zai gyaru.

Ministan ya alaƙanta rashin wutar da ake fama da shi, da matsalolin da ake fuskanta a cibiyoyin tura wutar lantarki guda takwas na ƙasar.

Sannan ya ce an rufe cibiyar wuta ta Jebba domin yin wasu gyare-gyare da a kan yi kowacce shekara.

Haka zalika ya bayyana wasu ciboyoyi bakwai da suka hada da Geregu da Sapele da Omotosho da Gbarain da Omuku da Paras da Alaoji da ya ce suna fama da ƙarancin iskar gas, yayin da da tashar samar da wuta daga ruwa ta Shiroro ke buƙatar gyara.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *