Najeriya Na Buƙatar Maƙudan Kuɗaɗe Domin Yaƙi Da Zazzaɓin Cizon Sauro A Ƙasar- Ministan Lafiya

Najeriya Na Bukatar N1.89trn Don Yaki da Zazzabin Cizon Sauro Amma Babu Kudi-

Ministan lafiya a Najeriya bayyana buƙatar makuɗan kuɗaɗe domin yaƙi da zazzabin cizon sauro

Ministan ya yarda ƙasar ba ta isassun kuɗaɗe duba da yadda annobar korona ta lalata tattalin arziki. Ya kirayi ƙungiyoyi da su tallafawa gwamnati wajen yaƙi da zazzaɓin na cizon sauro a ƙasar, Najeriya na buƙatar sama da naira tiriliyan guda domin yaki da zazzabin cizon sauro a kasar, in ji Dokta Osagie Ehanire, gidan Talabijin na Channels ta ruwaito. Ya bayyana cewa daga cikin jimillar kuɗin, kasar na bukatar sama da naira biliyan 350 don yaki da cutar a shekarar 2021 kadai. Ministan Lafiya, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *