Sharudan da Man United ta san yawa Ronaldo idan ya na son dawo wa.

Ƙungiyar kwallan kafa ta Manchester United ta sanarwa da Cristiano Ronaldo cewa idan har yanaso ya da wo zuwa tawagar to dole ya rage yawan albashin da zai rika karba kamar yadda Gazzetta dello Sport ta rawaito.

Mai shekaru 35 Ronaldo makomarsa a tawagar da ke kasar Italiya ba ta da tabbas kawo yanzu tun bayan ficewa da sukai a gasar kofin zakarun turai a hannun FC Porto.

Haka zalika kawo yanzu a gasar Serie A Juventus ta na kasan mai rike da mataki na farko Inter Milan da ta zarar maki 11 bayan da ya rage wasanni shida kacal a kammmala kakar wasanni ta bana.

Manchester United dai tuni ta fara shirin dawo da tsohon dan wasanta da akan kudi Yuro Miliyan 26.

Ko Yuro Miliyan 30 domin dawo warsa filin wasa na Old Trafford, bayan wata ganawa da suka fara da Wakilin dan wasan Jorge Mendes a makon da ya ga bata.

Rahoto: Ahmad Hamisu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *