Sunday Igboho ya sha dakyar a hannun wasu ‘yan bindiga

Shahararren mai nuna kyama ga al’ummar Fulani da Hausawa a jahohin kudancin Najeriya Sunday Igboho ya sha dakyar a hannun ‘yan bindiga a lokacin da suka kai wa gidansa farmaki.

Rahotanni sun bayyana Sunday Igboho ya yi nasarar haurawa ta katangar gidansa a lokacin da ‘yan bindigar ke bata kashi da masu gadin gidan sa ne.

Sai dai masu gadin gidan sun dora alhakin kai harin ga gwamnatin Najeriya ne karkashin jagorancin shugaba Buhari.

Saboda haka sun gargadi gwamnatin Najeriya data kiyaye farmakar uban gidan su ko kuma a samu gagarumar matsala.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *