Tsohon Gwamnan Imo Rochas Okorocha Baya Hannunmu, “Cewar Hukumar EFCC”

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta tabbatar da cewa yanzu haka tsohon gwamnan jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha baya hannun ta.

Idan zaku tun sanatan da ke wakiltar mazabar Imo ta yamma a majalisar dattijai yana tsare a ofishin EFCC da ke Abuja tun ranar Talata 14 ga Afrilu, kan batutuwan da ke damun sa game da zargin rashawa.

Gwamnatin jihar Imo ta zargi tsohon gwamnan da ayyukan cin hanci da rashawa da dama ciki har da karkatar da kudaden jama’a, zargin da ya sha musantawa.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis 15 ga Afrilu, ta ce Sanatan da ke wakiltar Gundumar Sanatan Imo ta Yamma ya bar ofishin Hukumar a yammacin ranar Alhamis, 15 ga Afrilu, 2021.

Sam Onwuemeodo, mai ba Okorocha shawara kan harkokin yada labarai ya kuma tabbatar da cewa ya bar Ofishin Hukumar Yaki da Rashawa a ranar Alhamis.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *