Uncategorized

‘Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, sun kashe mutane 7, sun sace 57.

Spread the love

Akalla mutane bakwai ne aka ruwaito an kashe tare da yin garkuwa da 57 biyo bayan wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai hari kan wata mota a Kuriga da ke kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna a ranar Asabar.

Wani dalibin Sakandaren Kimiyya na Gwamnati a Birnin-Gwari, an ce ya tsere da harbin bindiga.

Shugaban kungiyar Birnin Gwari Vanguard mai kula da harkokin tsaro da shugabanci nagari, Ibrahim Nagwari, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce ‘yan bindigar sun kuma kai hari a Unguwar Bula, Unguwar Dafillo da Ijinga a yankin Randagi na karamar hukumar.

“Yau, da misalin karfe 10:00 na safe, wani dalibin shekarar karshe na Sakandaren Kimiyya dake Birnin-Gwari ya tsallake rijiya da baya da harbin bindiga a kafadar sa akan hanyar sa ta yin rijistar JAMB/UMTE a Kaduna.” Inji sanarwar.

“ ‘Yan bindiga sun yi ta harbe-harbe a kan motar da ke dauke da daliban a kauyen Manini bayan Kuriga da ke kan titin Birnin-Gwari Kaduna.

“Dalibin yana jiran a yi masa tiyata a cire harsashin a kafadarsa a babban asibitin Jibrin Maigwari da ke Birnin-Gwari.

“Hakazalika, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kashe mutane bakwai a Unguwar Bula, Unguwar Dafillo da Ijinga a gundumar Randagi, a Birnin-Gwari ranar Asabar.

“’Yan bindigar da ke kan motoci sun kai hari a kauyukan da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a kuma sun dauki tsawon awanni hudu suna hana mutane gudanar da sallar Juma’a.

“’Yan bindigar, baya ga kashe mutum shida a nan take, wani mutum kuma ya mutu a safiyar yau a babban asibitin Jibrin Maigwari, yayin da suka sace mutane 57 suka yi garkuwa da su, yawancinsu mata ne ‘yan unguwa daya.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button