Uncategorized

Zamu ci zabe ko ta halin ƙaƙa a Kano a 2023 – Abdullahi Abbas

Spread the love

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi barazanar samun kuri’un Kano ta ko ta wacce hanya a zaben gwamna na 2023 mai zuwa a jihar.

Da yake jawabi ga ‘yan jam’iyyar a wajen yakin neman zaben jam’iyyar APC a Gaya, Kano, a ranar Laraba, Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar a jihar, ya ce ba zai yi sanya ba kan barazanar kwace Kano a zabe mai zuwa.

“Mutane na cewa in daina cewa APC za ta kwace Kano ko ta halin ƙaƙa. Ina so in shaida wa wannan taron cewa APC za ta kwace Kano da ta kowacce hanya, in ji Mista Abbas.

Ya kara da cewa “a yau mun nuna kudurinmu na cin zabe tun daga sama har kasa a shekarar 2023.”

Da yake karin haske a wurin yakin neman zaben, Mista Abbas ya ce “Gaya, kamar yadda kuka sani, gidan APC ne; babu wata jam’iyyar siyasa da za ta yi daidai da karfinmu.

“Mun kuduri aniyar daukar bijimi da ƙaho domin ci gaba da mulkin mu. Gawuna shi ne dan takararmu kuma shi ne zai zama gwamnan jihar Kano.”

A zaben gwamna na 2019 a jihar, gwamna mai ci Abdullahi Ganduje ya kusa shan kaye a hannun ‘yan adawa kafin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa zaben bai kammalu ba.

Mista Ganduje na jam’iyyar APC mai mulki ya ci gaba da lashe zaben da aka sake gudanarwa, inda ya doke dan takarar jam’iyyar PDP da ‘yar tazara.

PG

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button