Zan kawo karshen matsalar Talauci da rashin tsaro idan aka zabe ni shugaban kasar Nageriya – Inji Peter Obi.

Obi ya yi wannan alkawarin ne a wani gangami da kungiyar Middle Belt Forum ta shirya a ranar Alhamis a Jos.

Dan takarar jam’iyyar LP, wanda ya kuma yi alkawarin magance yunwa, rashin aikin yi da cin hanci da rashawa, ya ce zai inganta harkar ilimi a dukkan matakai da inganta samar da wutar lantarki.

“Idan kuka zabe ni a matsayin shugaban ku, zan kawo karshen samar da tsaro a kowane mataki ta yadda mutanenmu za su yi noma kuma ta yin hakan, matsalar karancin abinci da yunwa za ta zama tarihi.

“Za mu samar da ayyukan yi ga matasa marasa aikin yi da kuma kawo karshen talauci.

Za mu sanya tsarin ilimin mu ya yi aiki da inganta samar da wutar lantarki.

“Za mu toshe duk wani liki da kuma kawo karshen cin hanci da rashawa a kowane mataki; gwamnatinmu za ta zama mai alhaki. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba.

“Muna son sabuwar Najeriya kuma mun kuduri aniyar sake farantawa ‘yan Najeriya rai,” in ji shi.

Obi, ya shawarci jama’a da su yi addu’ar samun zabe mai inganci a shekarar 2023, inda ya kara da cewa sahihin zabe ne kadai zai samar da sahihin shugabanni.

Tun da farko, Dr Pogu Bitrus, shugaban kungiyar Middle Belt Forum, ya ce dandalin na goyon bayan takarar Obi, yana mai jaddada cewa shugabancin Obi zai magance matsalolin da ake fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *