Labarai

Uwar Gidan Gwamna El’rufa’i ta shirya gasa a Kan yaki da cutar kansa.

Spread the love

A daidai lokacin da aka cika kwanaki 16 da fara gwagwarmayar yaƙi da matsalar fyaɗe da cin zarafin ƴaƴa mata da yara ƙanana wacce aka fara (daga ranar 25 ga watan Nobemba zuwa 10 ga watan Disamba, 2020) uwar gidan gwamnan Jihar Kaduna, Ummi Garba El’Ru’i, ta haɗa gasa mai taken: #ummielrufaisgbvchallenge!

“Akwai buƙatar gaba ɗayanmu tare da jarumai mu mara baya akan yaƙi da matsalar cin zarafin jinsi saboda yaranmu ƙanana maza da mata da ƴan mata da mutane masu buƙata ta musamman, gaba ɗaya su na buƙatar kariya”. Inji Aisha-Ummi El-Rufai

Gasar ƙalubalen wacce ta jawo hankali matuƙa a sabbin kafafen sadarwa na zamani, ta buƙaci al’umma su bazu a wuraren da su ke rayuwa su dauki bidiyo na mintuna 2:30 suna wayar da kan jama’a kan abunda ya kamata su sani kuma su yi a lokacin da aka samu hatsarin fyaɗe, su yi bayani akan hatsarin da kuma bada hanyoyin kariya kan fafutukar yaƙi da matsalar wajen bincike da hannata lamarin ga rundunar tsaro.

A ƙarshen gasar ƙalubalen mai taken: #ummielrufaisgbvchallenge, uwar gidan gwamnan ta bayar da kyautar kuɗade ga waɗanda su ka lashe gasar kamar haka:-

Wanda ya zamo na ɗaya su ne: @team_nonstop (a Instagram) tawagar da ta haɗa da:
@musab_jibril
@maamah.hussein
@siryunus_ibrahim
Sun samu kyautar Naira Dubu Dari Biyar da Hamsin (N550,000)!.

Wadda ta zo na biyu ita ce Amina Zakari @ummeeytarh (a Instagram) inda ta samu kyautar Naira Dubu Dari Uku da Hamsin (N350,000)!.

Sai waɗanda su ka zo na uku, su ne Marie White da Reuben Victoria inda kowanensu su ya samu kyautar Naira Dubu Dari Biyu da Hamsin (N250,000). Marie White (a Facebook), Vicky_ru (a Instgram).

“Mu na matuƙar alfahari da ku, mu na fatan ƙwazonku zai cigaba da taimakawa wajen wayar da kan jama’a game da yaƙi da matsalar fyaɗe da sauran nau’ikan cin zarafi”. Inji Aisha-Ummi Garba El-Rufa’i, matar gwamnan jihar Kaduna.

Ummi ta kuma yabawa ƙwazon duk waɗanda su ka fafata a gasar ta neman jawo hankalin jama’a a mara baya kan yaƙi da matsalar fyaɗe da sauran dangogin cin zarafin mutane musamman mata da ƙananan yara.

Baya da haka, ta kuma ƙara da baiwa wasu daga cikin waɗanda su ka taka rawa kyautar lambar yabo ta kuɗi domin ƙarfafa musu gwiwa. Kowane mutum ɗaya ta bashi Naira Dubu Dari-Dari (N100,000). Mutanen da ta ba wa sun haɗa da:

  • BeeJayzphotos (Facebook)
  • Aysha Ahmad ~ elgashash
    Musa Sa’ad (Instagram)
  • Shamzik Care Foundation (Instagram)
  • Blessing Okebugwu (Instagram)
    @blessingOkebug2 (Twitter)

*Bello idris (Instagram)
@belloyombi (Twitter).

Sai kuma wadda ta taka rawa na musamman Pamelagold Ojoma Hassan; wacce bidiyon da ta samar ya fi na kowa ta samu Naira (N200,000)! o.j.o.m.a_ (Instagram).

“Mu na matuƙar alfahari da ku, sannan mu na fatan za ku kasance abokan hulɗarmu wajen yaɗa ɗumbin saƙonni a nan gaba”. Inji ta.

Daga ƙarshe ta kuma yi godiya da yabawa da ƙwazon kwamitin alƙalan gasar da ta kafa waɗanda ta jagoranta:
UNFPA (@unfpakd)

Mariama Darboe, jagorara shirye-shirye ta UNFPA na Kaduna Kaduna – (@mariamaDarboe18)

Hafsat Kagara, mai ba da shawara ta fannin shari’a a UNFPA kan yaƙi da mtsalar fyaɗe da cin zarafi a Jihar Kaduna (@kagara_hafsy).

Professor Hauwa Evelyn Yusuf, Farfesa akan ilimin jinsi da binciken gano masu laifi (Criminology and Gender Studies, KASU – (@ProfHEY1).

Madam Juliana Joseph – (@SalamaSarc) manajar cibiyar. Salama SARC.

Adejoke Fayemi, shugaban sashe (Head of Station, Raypower – (@favouredjoke)

Dakta Binta Kasim Mohammed, Associate Professor of Mass Communication, KASU – (@Bazazzaga)

Dakta Zubaida Abubakar, Gender/GBV Specialist UNFPA Nigeria – (@ab_zubaida).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button