Uwar Jam’iya ta Kasa tayi fatali da Zaben shugabanin tsagin Aminu Wali A jihar Kano.
Jam’iyyar PDP ta kasa tayi watsi da zaben shugabanninta na Kano, da bangaren Amb Aminu Wali da Sanata Bello Hayatu Gwarzo suka gudanar a jiya 17/12/2020, yayin da karbi na tsagin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya gudana ranar 14/12/2020, inda aka zabi Shehu Wada Sagagi, a matsayin shugaba, da sauran masu taimaka masa.
Cikin sanarwar da PDP ta fitar, mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaranta, Kola Ologbondiyan, yace anbi ka’idar jam’iyya a zaben nasu Kwankwaso, kuma anbi ka’idar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, wannan ke nuna cewa Shehu Wada Sagagi, na tsagin Kwankwaso, da sauran shugabanni zasu yi shekaru hudu suna rike da jam’iyyar, kamar yadda yake a kundun tsarin mulkin jam’iyyar.
Ka zalika, shima zaben shugabancin jam’iyyar PDP na kananan hukumomi 44, an karbi na tsagin Sanata Kwankwaso, wanda suka gudanar a ranar 12/12/2020, kamar yadda tsarin jam’iyyar yake, cikin dokar da aka yiwa kwaskwarima a shekarar 2017, da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa.
A karshe, PDP tayi kira da masu ruwa da tsaki da sauran ‘ya’yanta dake Kano, dasu bada goyon baya ga sabon shugabancin karkashin Sagagi, domin dorewar cigaban jam’iyyar da kuma cigaban Nigeria baki daya.
Daga: Kano Online News
18/12/2020