Rahotanni

Wa’adin Da Hukumar Karota Ta Jihar Kano Ta Bawa Masu Sana’a A Gefen Titin Kasuwar Sabon Gari Ya Cika.

Spread the love

Jiya da misalin karfe dayan dare zuwa biyun dare hukumar karota ta jihar kano ta fara rushe rumfunan da ke gefen titin kasuwar sabon gari bayan da wa adin data basu yacika.

Rusau din da hukumar karotar ta fara a Daren jiya ya faro ne tun daga kan masu sana a a karkashin sabuwar gadar da gwamnatin kano ta kammala Wanda ya hada Dana gefen kasuwar sabon gari, kasuwar singa da duk hanyoyin da sabuwar gadar ta biyo.

Masu rumfunan sun wayi gari sunje sun tarar da duk an rushe musu rumfunan bisa jagorancin shugaban hukumar karota ta jihar kano baffa babba Dan agundi.

Allah ya sawwake, Allah ya kawo mafita. Ameen.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button