Labarai

Wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke ciki a halin yanzu sun zama dole don ci gaban tattalin arziki – Tinubu

Spread the love

“Radadin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, sadaukarwa ne da ya kamata dukkan mu mu yi. Dukkanmu masu ruwa da tsaki ne a ci gaban al’ummarmu mai daraja,” in ji Mista Tinubu.

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta janye matsalar tattalin arzikin da suke fama da ita.

A ranar Laraba, Mista Tinubu ya ba da wannan tabbaci a Uyo a cikin wani sako a bude taron Editocin Najeriya (ANEC).

Shugaban wanda ya samu wakilcin ministan yada labarai Mohammed Idris, ya ce yana sane da wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki kuma ya dauki muhimman matakai domin dakile illolin cire tallafin man fetur.

Mista Tinubu ya lissafta kyautar N35,000 ga ma’aikatan gwamnati, da motocin safa na CNG na biliyan 100 da rattaba hannu kan wasu matakai guda biyar na inganta harkokin kasuwanci a matsayin wasu matakan da gwamnatin ta dauka.

Ya ce wasu sun hada da kokarin kawar da biliyoyin daloli da aka gada daga kudaden waje da kuma kafa kwamitin domin rage wa ‘yan Najeriya haraji.

“Radadin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, sadaukarwa ne da ya kamata dukkan mu mu yi. Dukkanmu masu ruwa da tsaki ne a ci gaban al’ummarmu mai daraja,” ya kara da cewa.

Mista Tinubu ya ci gaba da cewa gwamnatin ba ta huta ba amma tana kokarin ganin ta samu ci gaba da wadata. Ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta yi maraba da tattaunawa don ci gaban tattalin arzikin.

Shugaban ya umarci kafafen yada labarai da su tabbatar da gaskiya a cikin rahotannin al’amuran kasa.

Taken taron shi ne ‘Karfafa Ci gaban Tattalin Arziki, Ci gaban Fasaha: Matsayin Watsa Labarai’.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button