Siyasa

Wakilan Jam’iyyar PDP Sama Da 2,000 Ne Zasu Yi Zaben Fidda Gwani a Ondo.

Jam’iyyar Adawa ta PDP a Kasar Nan Tace mambobin Jam’iyyar Sama da 2000 ne zasu gudanar da Zaben Fidda Gwani na Gwamnan Jahar.

Sanarwar da Shugaban Jam’iyyar na Rikon Kwarya a Jahar Mista. Clement Faboyede ya Sanar, Yace Mambibin Jam’iyya sun Fitone daga Mazabu 203 da Kananan Hukumomi 18 na Jahar.

Faboyede yace “Munada ‘yan Takarar Gwamnan Jahar Guda 8 sannan Mun Cimma Yarjejeniya akan Duk wanda yaci zasu bashi hadin kai a tafi Tare.

Kwamitin zaben mai mambobi 5 wanda Gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi yake Jagoranta Suma za su sa Ido kan Zaben da Za’a Gudanar Gobe Laraba a Filin Taron Kasa da Kasa ta DOME Akure dake Babban Birnin Jahar.

Mai magana da yawun ‘Yan Sandan Jahar Mr. Teeleo Ikoro yaci alwashin zasu Tsaya Tsayin daka domin ganin Anyi zaben Lafiya an Gama lafiya Inji Shi.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button