Wakilin Da Yake Hanzari Wajen Sakuke Nauyin Da Al’ummarsa Suka Dora Masa..

Daga Sabiu Danmudi Alkanawi.
Salon Yadda Yake Gudanar Da Mulkinsa Abin Kwai-kwayo Ne Ga Duk Wani Jagora Nagari.
Salo Da Tsarinsa Yadda Yake Tafiyar Da Al’amuran Mulkinsa Dabara Ce Irin Wadda Magatanmu Nagari Sukayi Amfani Da Ita Kuma Sukayi Nasara.
Jajircewarsa Da Yadda Yake Kokari Wajen Tabbatar Da Ya Taimaki Mai Bukatar Taimako, Kai Da Gani Ka San Shi Ma’aikaci Ne.
Na San Mai Karatu Ya Kagu Yaji Ko Waye Wannan Naketa Yabonsa Haka?
Shine Eng. Abubakar Kabir Abubakar Bichi, Danmajalissar Tarayya Mai Wakiltar Bichi.
Ban Dade Da Saninshi Ba, Dan Lokacin Da Nafara Saninshi Shine Lokacin Da Kamalu Edita Bichi Yaturomin Da Case Din Rashin Lafiyar Usman Usman, Wanda Ake Neman Kudi Kimanin Naira Dubu Dari Biyi (N200,000), A Lokacin Nayiwa Shugaban Gidauniyar A.A Rano Foundation Abdallah M Abdallah Magana, Harma Naturasu Office Din A.A Rano Foundation Na Asibitin Nassarawa. Kafin Sugama Cika Ka’idojin Da A.A Rano Foundation Suke Bukata Sannan Subiya Kudin Aikin Sai Kamalu Edita Bichi Yakirani Yake Cemin Eng. Abubakar Kabir Abubakar Bichi Ya Tura Wakilansa Asibitin, Kuma Sun Bawa Mara Lafiyan Naira Dubu Dari Biyi Cash Domin Yabiya Kudin Aikin. Abin Ya Bani Mamaki, Saboda Yawancin ‘Yan Siyasarmu Alkawarin Yayewa Mutane Matsala Suka Iya, Amma Basu Iya Yaye Matsalar Ba.
Haka A Wannan Zaman Gidan Da Aka Fara A Kano Gab Da Azumi Na Sami Labarin Eng. Abubakar Abubakar Bichi Ya Rabawa Al’ummar Mazabarsa Kayan Abinci, Bayan Kwana Biyu Da Rabon Na Bincika Domin Na Tabbatar Da Sahihancin Rabon Da Yayi, Da Bincikena Yayi Nisa Sai Nasami Bayanin Cewa Ai Rabo Ma Yanzu Yafara, Dan Mazabu Mazabu Yaraba Aikin, Kowacce Mazaba An Ware Mata Tallafin Mutane Dari Biyu, Banda Ma Babbar Mazaba Ta Bichi, Wadda Ita Kayan Tallafinta Sunfi Yawa Saboda Yawan Al’ummarta.
A Kwanannan Ma Na Sami Labari Cewa Eng. Abubakar Kabir Abubakar Bichi Ya Kafa Wani Kwamiti Wanza Zai Zakulo Hanyoyin Magance Matsalar Ruwan Sha A Bichi.
Kadan Kenan Daga Cikin Abubuwan Da Nasani Game Dashi. Allah Yasaka Masa Da Mafificin Alkhairi, Allah Yaciga Da Yimasa Jagoranci, Allah Yabiya Masa Bukatunsa Na Alkhairi Amin.
Sabiu Danmudi Alkanawi..