Rahotanni
Walkiya Ta Kashe Jami’an Hukumar Lura Da Haddura Guda Uku A Jihar Ogun.
A jiya Laraba ne Wata Awlkiya da akayi ta kashe jami’ai uku na Hukumar Kula da Hanyoyi ta Tarayya da ke Rundunar Yankin Jihar Ogun.
Walkiyar ta riski Jami’an ne a ofishinsu da ke Ilese, a karamar hukumar Ijebu ta Arewa maso Yammacin jihar.
Laamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe lokacin da wadanda abin ya shafa ke shirin gabatarwar safiyar.
Akwai jami’ai sama da 10 a wurin da abin ya faru.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar reshen jihar Ogun, FRSC, Florence Okpe, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai Okpe ya ce har yanzu ba a tantance musabbabin mutuwar ba.