Wallahi Allah Maryam yahaya bata da mutunci Aliyu dahiru Aliyu
Wani matashi ya kwancema maryam yahaya zane a kasuwa inda Matashin mai suna Aliyu dahiru Aliyu yace Wallahi Allah Maryam Yahaya bata da mutunci. Ya mutum zai yi tattaki tun daga Yobe ya zo ganinki amma ki ki saurarsa? Wannan ai hauka ne da rashin sanin mutuncin masoyi. A ce saboda sonki har fiya-fiya bawan Allah ya sha amma ko a kula ta gagara?!
Idan yanzu kin ga kina tashe to ki tambayi yau ina Safiya Musa? Ina Fati Muhammed? Ko Mansura Isah da ta auri Sani Danja ina take yanzu? Ban da ma tana aiyukan tallafi wa zai tuno da labarinta? Su Hadiza Kabara kuwa yanzu rara-gefe suke. Duk wadannan an so su fiye da ke.
Yan wasan Hausan nan ku dauki kanku ku wani aza girman kan banza da wofi. Haka na ga wani mun shiga rastuwarent a Abuja yana ta wani kobarewa sai ka ce wata tsiya zai yi a gurin. Ke fa ba wani ilimi ne da ke na yabawa ba. Kudin ma wallahi babu. Sai dai hoto a Instagram da dan karan girman kan banza da wofi. In banda ma tuwo ya cika idon yaron ni sai na rasa me ya baro a Yobe ya tafi Kano kallon wannan yarinyar!
Shi masoyinka ai naka ne ko daga wani kauye yazo. Kin ganni nan wallahi zan iya haduwa da Messi ko Ronaldo ya yi gaba na yi gaba don basu dameni ba. Amma da muka hadu da Ali Nuhu a jirgi na ga mutane sun shareshi sai da na taso muka tattauna ko don na tuna masa shi “celebrity” ne da bai kamata a nuna masa bai isa ba. To bai kamata kuma idan kun shiga cikin jama’a ku dinga wulakanta wadanda suke nuna kun isa ba.