Wallahi Ba Ni Na Kona Takarduna Ba, Labarin Da Ake Yadawa Akaina Karya Ne, Abin Ya Tayarmin Da Hankali Matuka, Inji Matashi Auwal Usman.
Matashin da aka ce ya kona takardunsa saboda ya kasa samun aiki ya karyata labarin, inda yace labarin da ake yadawa karya ne.
Auwal Usman ya ce, “Anata Cece kuce a Gari, Hotuna na suna ta yyawo a kafafen yada labarai cewa ni Auwal Usman Matashin da ya Sadaukar da Bautar Kasar sa ga Uwar Gidan Shugaban Kasar Najeriya Hajjiya Aisha Buhari a Shekara ta 2019 na kona takarduna dan ban samu Aiki ba, Toh wannan zance ba gaskiya bane.
Ya kamata Mutane suyi watsi da wannan labarin.” Inji Auwal Usman
Auwal ya ce Takardunsa suna nan tare dashi.
“Ni ba mahauci bane da zan kona takardun da na Shafe shekaru goma sha ina wahala akansu,” inji shi.
Matashin ya ce labarin ya samo asali ne daga wani matashi mai suna sa Usman Abubakar, wanda sunansu ya kusan zuwa daya, shi sunan shi Auwal Usman, shi kuma wanda ya kona takardun nashi sunanshi Usman Abubakar, sai jama’a suketa saka hoton Auwal Usman suna yadawa.
Auwal Usman ya ce
“Dan Allah A taimaka da Sharing Domin Duniya ta Gane Gaskiya Labarin.”