Labarai
Wani alkali ya tura wata Mata Mai shayarwa Gidan Kaso a jihar Kano.
Wani Alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano da ke Upper Shari’a Court Goron Dutse ya Tura Hannatu Isa mai Shayarwa Gidan Yari, Sakamakon Mijinta Bashir Daja da yayi ƙarar ta kan cewa ta Ba shi ‘yar sa ‘yar Shekaru 11 tun da suka rabu tana Jaririya babu Abin da ya taɓa yi mata, Inji ta.
Dalilin kai ta Gidan yari shine Alƙali ya sanya ranar zuwa ba ta samu zuwa ba Saboda rashin lafiya ba tare da binciken gaskiyar ta ko akasin haka ba ya tura ta Gidan Kaso.
Yanzu haka ƙungiyar Rigar Yanci International, Ta Shiga cikin Maganar Domin Tabbatar da Wannan Baiwar Allah ta Samu ‘yanci.
Cikakken Rahoto na nan tafe.